Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano zata kawo karshen rikicin masarauta da ke addabar jihar

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa zata kawo karshen rikicin masarauta da yakici yaki cinyewa a jihar kusan shekaru biyu

Bayanin hakan ya fitone ta bakin kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya inda ya ce gwamnatin zata dauki matakai masu karfi domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito game da rikicin sarakunan biyu harma ya ce ana gab da warwarewa

Kwamishinan ya ƙara da cewa akwai yiwuwar wasu daga cikin masu ruwa da tsaki su janye da kansu, ko kuma a cimma matsayar sulhu bisa fahimtar juna.

Ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da dukkan ɓangarori, tare da mutunta doka, martabar masarautu, da muradun al’ummar Kano.

Dangane da sauya sheƙar gwamnan zuwa APC, Waiya ya ce hakan zai buɗe ƙofofi masu yawa ga jihar, musamman wajen samun tallafin tarayya a fannoni kamar ababen more rayuwa, lafiya, ilimi da jin ƙai.

A halin yanzu, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu na zaune a fadar Gidan Rumfa, yayin da Aminu Ado Bayero ke zaune a fadar Nassarawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!