Labaran Kano
Gwamnatin Kano zata sake gina hukumar jin dadin alhazai
Gwmanatin Kano zata sake gina hukumar jin dadin alhazai ta jiha don yin kafada-da-kafada da na zamani wajen gudanar da ayyukan Hajji da na Umar.
Matakin ya biyo bayan amincewa da dokar ta kafa hukumar gyaran fuska da wajen sake inganta harkokin ta.
Kwamishinan yada labarai na jihar Malam MuhammadGarba ne ya sanar da hakan a taron manema labarai jim kadan bayan kamala taron majalisar zartarwa ta jiha, yana mia cewa matakin ya biyo bayan amincewa da lasisi daga hukumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON.
Hukumar alhazai ta Kano zata dauki mazauna Saudiya ma’aikatan wucin gadi
Hukumar jin dadin alhazai ta yiwa maniyyata hajjin bana na Kaduna 2,200 gwajin daukar bayanai
Kasar Saudiya ta tsayar da 3 ga Maris shekara ta 2019 a matsayin ranar rufe karbar adadin alhazai
Malam Muhammad Garba ya sanarwar da cewar nan bada jimawa majalisar zartarwa zata aike wa majalisar dokoki ta jiha kunshin gyaran don fara aiki da shi.
Gyaran fuskar da aka yi wa dokar hukumar jin dadin alhazan sun hada da kafa sashin yada ilimin addinin musulunci da wayar da kai da kuma kirkiro da sahshin shari’a don tabbatar da an gudanar da ayyukan Hajji da Umar yadda ya dace.