Labaran Kano
Gwamnatin Kano zata zaunar da makiyaya guri daya
Shirin bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano , wato ‘Kano state Agro Pastoral Development Project (KSADP)’, da Bankin Musulunci ke daukar nauyi , ya sha alwashin yin hanyoyi da Makarantu tare da Asibitoci da sauran aiyyukan bunkasa al’umma a kauyukan jihar Kano don tsugunar da makiyaya guri daya.
Shugaban shirin Malam Ibrahim Garba Muhammad Gama , ne ya bayyana haka ga Freedom Radio a ofishin hukumar tare da karin haske dangane da yadda aikin zai gudana a jihar Kano.
Ibrahim Garba Muhammad , ya kara dacewa shirin zai kafa manyan cibiyoyi na tattara Madara da Adana ta guda dari biyu (200), don inganta madarar a hannu daya kuma tare da samar da kasuwa ga Makiyayan cikin sauki ba tare da yawon tallace tallace ba.
Labarai masu alaka.
Gwamantin Kano ta kaddamar da kwamitin bunkasa harkokin noma
Bankin CBN ya bawa manoma bashi a Kano
Babban jami’in ya ce, shirin zai bada tallafi ga kananan mutanen Karkara musamman mata , da basu horo na yadda zasu gudanar da tsarin tara Madara ta hanyar Zamani , da samar da noman ciyawar bunkasa Nonon Shanu , a gefe daya tare da bunkasa Filin Noma na Watari don amfanar da manoma sama da dubu hudu (4, 000).
Shirin wanda zai gudana a tsawon shekara biyar , zai bada muhimmanci wajen inganta ,Noman Dawa, Masara da Gero da ciyawar bunkasa Nonon Shanu da Duba lafiyar Shanu tare da yi musu baye da Allurorin Rigakafi.
You must be logged in to post a comment Login