Connect with us

Labarai

Gwamnatin Katsina ta fara shirin samar da cibiyar kula da masu fama da cutar kansa

Published

on

Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da samar da cibiyar kula da masu fama da cutar kansa a Asibitin kwararru na Janar Amadi Rimi da ke jihar.

 

Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar aka kuma rabawa manema labarai.

 

Ya ce majalisar zartarwar jihar ta amince da shirin ne a zamanta na 19 na shekarar 2026, wanda aka gudanar ranar Juma’a a Gidan Janar Muhammadu Buhari da ke Katsina.

 

Sanarwar ta kara da cewa Kwamishinan Lafiya na jihar Musa Adamu, ya ce za a sauya cibiyar daukar hotunan cututtuka da gwaje-gwajen lafiya da ake ginawa a asibitin zuwa cibiyar kula da cututtuka daban-daban, ciki har da cutar kansa.

 

Kwamishinan ya bayyana cewa cibiyar za ta taimaka wajen gudanar da gwaje-gwaje na musamman da kuma samar da ingantattun hanyoyin kula da masu fama da cutar kansa a jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!