Connect with us

Labarai

Majalisar Wakilai ta fara bincike kan zargin matsalolin sarrafa kudade a jami’o’i

Published

on

Shugaban kwamitin kula da harkokin ilimin jami’o’i na majalisar Wakilai, Abubakar Fulata, ya jagoranci kaddamar da bincike kan zargin samun matsalolin sarrafa kudaden gwamnati a jami’o’in tarayya guda tara da wasu manyan makarantun gaba da sakandare.

 

Kwamitin ya bukaci shugabannin jami’o’in da abin ya shafa da su yi cikakken bayani kan yadda suke kashe kudaden da gwamnati ke ware musu.

 

kwamitin ya umarci shugabar Jami’ar Legas, Farfesa  folashade  Ogunsola, da ta gabatar da bayanan kasafin kudin jami’ar na shekarun 2024, 2025 da 2026, tare da bayyana a gabansa mako mai zuwa.

 

Hakan dai ya biyo bayan zargin samun sabanin naira biliyan bakwai da miliyan dari a bayanan kudaden jami’ar, lamarin da ya sa kwamitin ke neman karin bayani daga mahukuntan jami’ar.

 

Kwamitin ya ce ana bukatar bayanan ne domin tabbatar da yadda aka sarrafa kudaden gwamnati da kuma bin ka’idojin gudanar da harkokin kudi a cibiyoyin ilimi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!