Labarai
Gwamnatin Katsina ta sanya dokoki a kan Fetur da POS da cajin waya a Matazu da Musawa

Gwamnatin Jihar Katsina ta haramta saye, sayarwa, jigila da ajiye man fetur a jarkoki a fadin jihar tare da rufe sana’ar POS da wuraren cajin waya a Kananan Hukumomin Matazu da Musawa.
Hakan na cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a Daren jiya Litinin.
Sanarwar ta ce Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya amince da sabbin matakan bayan wani taron gaggawa kan tsaro da ya hada hukumomin tsaro, sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya kara da cewar an dauki matakan ne domin dakile ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane, bayan binciken tsaro ya nuna cewa masu aikata laifuka na amfani da man fetur, POS da wuraren cajin waya wajen gudanar da ta’ asar su
Gwamnatin jihar ta kuma haramta amfani da babura a Kananan Hukumomin Matazu da Musawa domin rage zirga-zirgar masu aikata laifuka a yankunan.
You must be logged in to post a comment Login