Labarai
Kotu ta umarci INEC ta soke rajistar ADC da wasu Jam’iyyu 4

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci hukumar zaɓe ta Najeriya INEC da ta soke rajistar jam’iyyu biyar da suka haɗa da African Democratic Congress ADC, bisa zargin gaza cika wasu sharuɗɗan da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada ga jam’iyyun siyasa.
Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, inda ya ce jam’iyyun sun kasa samun akalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da doka ta tanada a zaɓukan da suka gabata.
Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da ADC, Accord A, Action Alliance AA, Action Peoples Party APP da Zenith Labour Party ZLP.
Kotun ta kuma umarci INEC da kada ta bari waɗannan jam’iyyu su shiga zaɓuka masu zuwa, ciki har da babban zaɓen shekarar 2027, matuƙar ba a samu sauyi a shari’ar ba.
Wata ƙungiya mai suna Incorporated Trustees of the National Forum of Former Legislators ce ta shigar da ƙarar, tana mai zargin jam’iyyun da gaza cika sharuddan da suka shafi yaɗuwar tasirin siyasa da kuma sakamakon zaɓe kamar yadda doka ta tanada.
Ƙungiyar ta buƙaci kotun da ta umarci soke rajistar jam’iyyun, tana mai cewa ba su gabatar da hujjojin da za su karya zarge-zargen da ake musu ba.
Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da shirye-shiryen siyasa ke ƙara ƙamari gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
You must be logged in to post a comment Login