Labarai
Kaduna: Ƴan Sanda sun kama mutane 12 da ake zargi da satar mutane

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutane 12 da ake zargi da garkuwa da mutane tare da kwato bindigogi kirar AK-47 da miyagun kwayoyi a jihar.
Hakan na cikin bayanin da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Mansur Hassan, ya fitar a yau Talata.
Ya ce rundunar ta samu nasarar kama mutane 12 da ake zargi da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
Mansur Hassan ya ce jami’an rundunar sun kuma kwato bindigogi kirar AK-47 da kwayoyin Tramadol guda 2,700.
Ya kara da cewa an kwato motoci guda hudu a yayin aikin da jami’an tsaron suka gudanar.
You must be logged in to post a comment Login