Labaran Kano
Gwamnatin mu na kokarin inganta tsaro- Buhari
Shugaban kasa Muhammad Buhari , ya jaddada kudirin gwamnatin sa na inganta tsaro ,tare da tattalin arziki na kasa ,da kuma yaki da cin hanci don bunkasa tare da cigaba kasar nan.
Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne a yau wajen bikin yaye mataimakan Sufurtandan ‘yansanda na kasa wato ASP karo na biyu, su 628 da akayi a jami’ar yansanda dake garin Wudil.
Shugaba Buhari , ya kara da cewa kasancewar jami’an ‘yan sanda na daga cikin kashin bayan samar da tsaro a kasa, aikin samar da tsaro tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a ya ta’allaka ne kacokan kan Samar da kwararru kuma masu ilimi, da za su yi dai-dai da tsarin zamantakewar kasar nan mai al’umma daban -daban.
Shugaba Buhari ya bada umarnin tsas-tsaura matakan tsaro a jihar Borno
Shugaba Buhari ya bukaci manyan hafsoshin tsaro su kara jajircewa akan aikin su
Shugaba Buhari zai gudanar da taro kan lamuran tsaro a fadar Asorok
A nashi jawabin, Kwamandan Makarantar , AIG Zanna Ibrahim, ya ce duk da makarantar na fuskantar kalubale na dakunan dalibai da Ajujuwan Karatu, da sauran wasu matsalolin hakan ba zai sa suti kasa a gwiwa ba wajen, samar da kwararrun ‘yan sandan da zasu yi kafada da kafada da takwarorin su na sauran kasashen duniya da suka cigaba.
Wakilin mu na fadar gwamnatin jiha Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa daga cikin wadanda suka halarci wajen taron yayewar a yau , akwai gwamnan jihar Kano , Dr Abdullahi Umar Ganduje, ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Mai Gari Dingyadi, ,shugaban hukumar lura da ‘yan sanda , Musiliu Smith, sai Babban Sufeton yan sanda na kasa , Muhammad Adamu, da sauran iyalai da abokanan arzikin wadanda aka yaye a yau.