Labarai
Gwamnatin Neja ta sanya dokar hana fita a Ƙaramar Hukumar Rafi

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sanya dokar hana fita a yankunan da rikicin Kamuku da Fulani ya shafa a Ƙaramar Hukumar Rafi domin dawo da zaman lafiya.
Hakan na kunshe cikin sanarwar da Sakatariyar Yaɗa Labaran Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Ummikhaltume Abdullahi Kuta, ta fitar a Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan, wanda Mataimakin sa Yakubu Garba ya wakilta, ya kai ziyarar tantance ɓarnar da rikicin ya haifar, inda ya umarci shugabannin hukumomin tsaro su tura jami’ansu tare da ɗaukar matakan gaggawa domin dakile rikicin.
Sanarwar ta ƙara da cewa binciken farko ya nuna rikicin ya samo asali ne daga saɓanin noma da ya fara kusan watanni biyu da suka gabata.
Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya umarci Sarkin Kagara da ya kafa Kwamitin Sulhu da Sasanci domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin al’ummomin.
Haka zalika, gwamnatin jihar ta buƙaci masu amfani da kafafen sada zumunta su guji yaɗa bayanan da ba a tantance ba, tare da tabbatar wa mazauna yankunan da rikicin ya shafa cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare rayukan su da dukiyoyin su.
You must be logged in to post a comment Login