Connect with us

Labarai

Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da jefa mutane cikin yunwa

Published

on

Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jefa al’ummar kasar nan  cikin matsananciyar yunwa sakamakon gazawar manufofinta da kuma rashin shawo kan matsalar tsaro.

 

Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar na ƙasa, Malam Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar  da ya fitar a jiya Litinin.

 

Sanarwar ta bayyana cewa jam’iyyar ta yi wannan zargin ne bayan rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya, WFP, wanda ya nuna cewa mutane sama da miliyan 17 a jihohin Arewa tara na fama da matsananciyar yunwa.

 

ADC  ta ce hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda kan manoma, da tsadar rayuwa, sun ƙara ta’azzara matsalar.

 

Sanarwar ta ce  gwamnatin Tinubu ta gaza kare rayuka da dukiyoyin manoma, tana mai cewa matsalar yunwar da ake fama da ita ba ta samo asali daga ibtilaʼi ba, illa sakamakon gazawar gwamnati.

 

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa idan ta samu damar mulki za ta bai wa noma da samar da wadataccen abinci fifiko, tare da aiwatar da manufofin da za su ƙara yawan amfanin gona da rage tsadar abinci a faɗin ƙasar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!