Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta kama gurɓatattun kayayyaki na fiye da miliyan 300

Published

on

Gwamnatin Kano ta ce ta kama gurɓatattun kayayyakin abinci da abin sha da darajarsu ta haura naira miliyan 300 cikin ƙasa da watanni huɗu, yayin da wasu daga cikin ƴan kasuwar jihar ke ƙoƙarin sayar da su ga jama’a.

Shugaban Hukumar kare haƙƙin masu saye da sayarwa ta jihar Dakta Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana hakan yayin da yake bajekolin kayan da hukumar ta kama ga manema labarai.

Dakta Ibrahim Garba ya ce, kayayyakin da aka kama sun haɗa da waɗanda wa’adin amfaninsu ya ƙare da kuma waɗanda aka adana ba bisa ƙa’ida ba da wadanda jabu ne, lamarin da ka iya jefa rayuwar al’umma cikin haɗari idan aka bari aka sayar da su.

Dakta Garba ya ƙara da cewa, hukumar ta ƙara zage dantse wajen yin sintiri da bincike a kasuwanni da wuraren ajiyar kayan ‘yan kasuwa domin gano masu safarar gurɓatattun kayayyaki, tare da ɗaukar matakan doka a kansu.

Haka kuma, ya yi kira ga ƴan kasuwa da su guji sayar da kayan da ka iya cutar da lafiyar jama’a, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da hannu a irin laifukan , tare da bukatar al’umma su riƙa duba inganci da wa’adin amfani da kowane kaya da suke saya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!