Connect with us

Labarai

Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da fetur da gas zuwa ƙetare

Published

on

Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje.

 

Wannan matakin na zuwa a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin mai a gidajen man babban birnin ƙasar Yamai da ma wasu biranen ƙasar.

 

Ministan Ciniki da Masana’antu na Jamhuriyar Nijar, Abdoulaye Seydou, ya rattaba hannu kan wata doka da ta haramta fitar da man fetur da man gas daga ƙasar zuwa ƙasashen waje.

 

Kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP, ya ruwaito cewa gwamnatin Nijar ta ɗauki wannan matakin ne domin aiki da wata doka da ta buƙaci wadata ƙasar da makamashin man fetur da gas kafin a sayar wa ƙasashen duniya.

 

Dokar ta ce idan aka samu rara ta man gas da man fetur, matatar man Nijar SORAZ da kamfanin man ƙasar SONIDEP za su iya fitar da rarar ne kawai bayan sun samu izini na musamman daga ministan da ke kula da cinikayya na ƙasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!