Connect with us

Labarai

Ministan Ilimi ya buƙaci shugabannin jami’o’i su tabbatar da biyan ma’aikata albashi da alawus

Published

on

Ministan Ilimi na Najeriya, Tunji Alausa, ya buƙaci shugabannin jami’o’in gwamnatin tarayya da su tabbatar da biyan ma’aikata alawus-alawus da albashinsu a kan lokaci, tare da kauce wa jinkiri.

Alausa ya bayyana hakan ne yayin ganawa da shugabannin jami’o’in, inda ya nuna damuwarsa kan ci gaba da samun jinkirin biyan wasu haƙƙoƙin ma’aikata, duk da matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka na magance matsalolin kuɗaɗen biyan bashin ga ma’aikatan.

Ministan ya ce gwamnati ta tuntubi Ma’aikatar Kuɗi da sauran hukumomin da abin ya shafa domin biyan bashin haƙƙoƙin ma’aikata, inda ya bayyana cewa an biya wasu daga cikin bashin har zuwa watan Satumban shekarar nan.

Ya kuma gargaɗi shugabannin jami’o’in da su tabbatar da cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka ware wa albashi da sauran haƙƙoƙin ma’aikata bisa manufar da aka ware su, yana mai jaddada muhimmancin gaskiya, riƙon amana da kyakkyawan tafiyar da kuɗaɗen gwamnati.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!