Connect with us

Labarai

ECOWAS da AES sun kaddamar da tattaunawar aiki a tsakaninsu

Published

on

Kungiyar ECOWAS da ta Kasashen Sahel watau AES sun kaddamar da tattaunawa ta aiki tsakaninsu domin ceto haɗin kan yankin, biyo bayan ficewar da kasashen Mali, Burkina Faso, da Jamhuriyar Nijar suka yi daga ECOWAS watanni 18 da suka wuce.

 

A yayin taron da suka gudanar a birnin Dakar na Senegal, wanda shine na farko a hukumance bayan da ƙasashen yankin Sahel 3 suka fice daga ECOWAS, ministocin harkokin wajen ɓangarorin biyu sun fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa, inda suka amince da kafa kwamitocin ƙwararru na musamman, waɗanda aka ɗora wa alhakin tsara daftarin tsarin haɗin kai da kasuwanci da tsaro.

 

An gudanar da tattaunawar ce ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin wajen Senegal, Cheikh Niang, wanda ya wakilci ECOWAS, da kuma Ministan Harkokin Wajen Burkina Faso, Karamoko Jean-Marie Traoré, wanda ya wakilci ƙungiyar AES.

 

Wakilan taron sun jaddada cewa wannan tattaunawa ba wai sasantawa ba ce don dawo da ƙasashen na Sahel cikin ƙungiyar ECOWAS, tsari ne na gudanar da zamantakewa a nan gaba.

 

Mayar da hankali da aka yi kan tsaron kan iyaka da kasuwanci ya zo ne a wani lokaci mai muhimmanci ga manyan ƙasashen yankin kamar Najeriya, wadda ke da iyaka mai cike da ƙalubale tsakaninta da Jamhuriyar Nijar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!