Labarai
An murkushe yunkurin juyin mulkin Gwamnatin Sojin Nijar

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi bayani kan harbe-harben da aka kwashe tsawon dare ana ji har zuwa wayeywar garin Asabar a Yamai, babban birnin kasar inda ta ce ta murƙushe yunƙurin bore da wasu sojoji suka yi.
Lamarin ya tayar da hankulan mazauna birnin tare da jawo hankalin ƙasashen duniya.
A cikin sanarwar da ya karanta ta gidan talabijin na gwamnati, ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Modi, ya ce kimanin ƙarfe 12:20 na dare wani rukuni na sojoji sun kutsa cikin sansanin soji na 101 da ke kusa da filin jirgin saman Diori Hamani a Yamai, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin abokan aikinsu.
Sai dai ya ce dakarun ƙasar sun yi gaggawar mayar da martani, inda suka dakile yunƙurin tare da dawo da doka da oda.
“Bayan jajircewar dakarun ƙasar, yanzu komai ya koma daidai kuma an murƙushe boren da suka so tayarwa,” in ji sanarwar gwamnatin.
Kafin wannan bayani daga gwamnati, babu tabbas kan asalin inda ake harbe-harben, kuma ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba.
Ministan bai kuma yi karin haske kan ko akwai wadanda suka rasa rai ko kuma wadanda suka ji rauni ba.
You must be logged in to post a comment Login