Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da mutum1060 da ake zargi da ta’addanci

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da mutum dubu daya da sittin da ake zargi da ta’addanci a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, a mataki na goma sha daya na shari’ar da ake yi wa wadanda ake zargi da aikata laifukan ta’addanci.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya ce a yau Juma’a kotun ta yanke wa mutum 653 hukunci, bayan ta saurari kararraki 880. Ya ce an kuma wanke mutum bakwai, yayin da aka sallami mutum 27 ba tare da yanke musu hukunci ba.

Fagbemi ya ce wannan shi ne mataki mafi girma tun bayan da gwamnatin tarayya ta fara shari’ar gama-gari kan wadanda ake zargi da ta’addanci. Ya danganta ci gaban da hadin gwiwar bangaren shari’a da hukumomin tsaro, da kuma kokarin lauyoyin masu gabatar da kara da na wadanda ake tuhuma.

Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da shari’ar, kuma za a sanar da cikakken adadin wadanda aka yanke wa hukunci bayan kammala ta. Ministan ya kara da cewa shirin gyara tunanin wadanda kotu ta amince da su, da taimaka musu wajen komawa cikin al’umma, na daga cikin matakan da ake dauka domin rage yiwuwar komawarsu aikata laifukan ta’addanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!