Connect with us

Labarai

APC ta zargi Atiku da ADC da shirin yada labaran karya kan gangamin Tinubu a Kaduna

Published

on

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya zargi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da jam’iyyar ADC da shirin yada labaran karya domin bata sunan gangamin yakin neman zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka shirya gudanarwa a Kaduna.

 

Mai magana da yawun kwamitin Dele Alake ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar 24 ga Oktoba, 2026, inda ya yi zargin cewa ana shirin amfani da farfaganda da kirkirarriyar fasahar AI, wajen yada bayanan da ba su da tushe.

 

Alake ya yi zargin cewa an karkatar da ma’anar hoton wata motar jami’an tsaro da ke sintiri a kusa da allunan tallan APC, domin nuna cewa jami’an na ba wa allunan tallan jam’iyyar kariya.

 

Ya kuma zargi Atiku da wasu magoya bayan ADC da yada wata wasika da ake zargin an kirkira, wadda aka ce ta kunshi bukatar sakin naira tiriliyan biyu da digo uku domin gudanar da gangamin kamfen ɗin APC a jihar Kaduna.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!