Labarai
Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi
Gwamnatin tarayya ta ayyana litinin na makon gobe a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidi da tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Salallahu Alaihi wasallam.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na ma’aikatar kula da harkokin cikin gida Muhammed Manga.
Sanarwar ta ruwaito ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola na ta ya al’ummar musulmin kasar nan murnar tunawa da ranar haihuwar ta fiyayyen halitta.
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kalaman da jam’iyyar PDP ke yi hutun shugaba Buhari
Babban jojin kotun tarayya ya fitar da jadawalin hutun manyan kotunan kasar nan
Ogbeni Rauf Aregbesola ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su rika koyi da halayyar fiyayyen halitta Annabin tsira Muhammadu Sallallahu alaihi wasallam, wajen hakuri da kuma juriya da juna.