Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta bai wa jihohi da cibiyoyin lafiya biliyan 32 -Minista Pate

Gwamnatin Tarayya, ta sanar da cewa za ta bai wa jihohi da cibiyoyin lafiya naira biliyan 32, kafin ƙarshen watan nan da muke ciki na Oktoba domin inganta kiwon lafiyar jama’a.
Ministan lafiya da walwalar Jama’a, farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Larabar makon nan bayan ƙaddamar da sabon tsarin BHCPF 2.0, wanda ke mayar da hankali kan gaskiya da inganci da biyan sakamako bisa aiki.
Tuni dai gwamnatin ta kaddamar da wasu tsare-tsare na wani asusu da aka tanada domin kula da harkokin lafiya a matakin farko da nufin tabbatar da cewa kuɗin da za a raba za a yi amfani da su yadda ya dace domin inganta ayyukan kiwon lafiya a faɗin Najeriya.
Ministan ya ce, ɗaukar matakin na da nasaba da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da gaskiya da amfani da kuɗaɗen gwamnati da na abokan hulɗa ta hanya mai inganci, da gwamnatin ta ce yawan cibiyoyin lafiya da ke amfana da kuɗin BHCPF zai ƙaru daga 8,800 zuwa 13,000.
You must be logged in to post a comment Login