ilimi
Gwamnatin Tarayya ta buɗe cibiyar bunƙasa fasahar zamani a Kano

Gwamnatin Tarayya, ta buɗe cibiyar bunƙasa fasahar zamani da ta gina a nan Kano domin ƙara buƙasa harkokin fasahar sadarwa a faɗin Najeriya.
Da ya ke jawabi yayin bude cibiyar, Ministan harkokin sadarwa Kirkire-kirkire da kuma bunkasa fasahar sadarwa Dakta Bosun Tijani ne ya wakilci Shugaban kasa Bola Ahmed wajen bude cibiyar a yau Laraba, inda ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe kudade masu yawa wajen gina cibiyar ta Digital Industrial Park da ke kan titin zuwa Gidan Gwamnatin Kano.
A nasajawabin, shugaban hukumar sadarwa ta ƙasa NCC, Dakta Aminu Maida, ya ce, cibiyar wadda ke karkashin hukumarsa, za ta gudanar da muhimman ayyuka da suka hadar da horas da matasa da koyar da ɗalibai da sauran aikace-aikace.
Da ya ke bayyana muhimmancin cibiyar, gwamnan Kano wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce, Gwamnatin tarayya ta samar da cibiyar ne la’akari da ɗimbin matasan da ke cikin harkokin fasaha a Kano.
Shi kuwa ministan ci gaban harkokin matasa Ayodele Olawande, ya yaba wa gwamnatin Kano da kuma gwamnatin tarayya bisa gyara cibiyar bayan da matasa suka lalata ta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa inda ya ce, ɗimbin matasan ƙasar nan za su ci gajiyar cibiyar.
You must be logged in to post a comment Login