Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta bukaci rufe asusun ajiyan banki guda biyar mallakin babban jojin kasa
Gwamnatin tarayya ta bukaci sashen kula da hada-hadar kudi ta kasa NFIU da ya rufe asusun ajiyan banki guda biyar mallakin babban jojin kasa Walter Samuel Onnoghen.
Attorney janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami ne ya ba da wannan umarni.
A cikin wata wasika mai dauke da sa hannun wani makusancin Attorney janar na kasa mai suna Abiodun Aikomo ta bukaci da a rufe asusun ajiyan har sai an kammala shari’ar da a ke yi ma sa a kotun da’ar ma’aikata.
A baya-bayan Nan ne dai aka gurfanar da babban jojin kasa Walter Samuel Onnoghen gaban kotu kan zargin sa da mallakar wasu asusun ajiya na banki guda biyar, wanda tun farko bai bayyana su cikin kadarorin da ya mallaka ba.