Labarai
Gwamnatin tarayya ta dage zaman majalisar zartaswa na gaggawa da za ta yi

An dage zaman majalisar zartaswa na gaggawa da shugaban kasa ya kira don nuna alhini ga rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da aka shirya gudanarwa a yau Talata.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya kira taron gaggawar ne a jiya wanda za a gudanar a yau, jim kadan bayan sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar tare da mayar da shi zuwa ranar Juma’a.
Dage taron yazo daidai da lokacin da za gudanar da jana’izar marigayin a mahaifarsa dake Daura shima a yau Talata.
Mai magana da yawun shugaban kasa kan kafafen yada labarai Bayo Onanugan ya ce za a kawo gawar shugaban a yammacin wannan rana.
You must be logged in to post a comment Login