Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta fara biyan mu bashin da muke bin ta – NARD
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa reshen jihar Kano ta ce gwamnatin tarayya ta fara biyan su kuɗaɗen da suke bin ta ba shi.
Ƙungiyar reshen asibitin Aminu Kano ce ta bayyana hakan ta bakin jami’in walwalar ƙungiyar Dakta Haruna Yakubu a zantawar sa da Freedom Radio ta cikin Labaran Mu leƙa mu gano.
“A yanzu gwamnatin tarayya ta fara biyan wasu daga cikin mu kuɗaɗen su na albashi da suke bi bashi, kuma tana ci gaba da tantancewa don kammala biya” in ji Dakta Haruna.
Likitan ya ce, “Mun cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan cewa za ta janye ƙarar da ta shigar da mu gaban kotun ɗa’ar ma’aikata, kuma za ta mayar da dukkanin jami’an lafiya tsarin biyan albashi na IPPIS”.
Dakta Haruna Yakubu ya kuma ce, tsawon wata biyu kenan gwamnatin tarayya ba ta ba su albashi ba, sakamakon ƙoƙarin ta na cika alƙawarin da ta ɗauka na cewa ba za ta bada albashi ga ma’aikatan da suke yajin aiki ba.
“Mun sha wahala matuƙa da rashin albashi, domin kuwa mafi yawan mu ba mu da wani aiki da muka dogara da shi sai aikin kula da lafiya” a cewar Dakta Haruna.
Wannan dai ya biyo bayan janye yajin aikin da ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta yi a ranar Litinin, wanda ta shafe sama da wata biyu tana gudanarwa sakamakon zargin cewa gwamnati ta ƙi biya musu buƙatun su.
You must be logged in to post a comment Login