Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta fitar da fiye da Biliyan 38 don inganta jami’o’i

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta fitar da naira biliyan 38 da miliyan 93 domin inganta jami’o’i da sauran manyan makarantun gwamnati 166 a faɗin Najeriya.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta bayyana cewa tallafin zai shafi jami’o’i 79, kwalejojin kimiyya da fasaha 46, da kuma kwalejojin horas da malamai 41.

 

Bayanin ma’aikatar ya nuna cewa jami’o’i za su samu naira biliyan 28.5, yayin da kwalejojin kimiyya da fasaha za su samu biliyan 5.8, sannan kwalejojin horas da malamai za su samu biliyan 4.7.

 

Gwamnatin ta ce an fitar da kuɗaɗen ne domin magance ƙarancin kayayyakin more rayuwa da inganta wuraren koyarwa, tare da cika wasu yarjejeniyoyin da ta cimma da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!