Connect with us

Labarai

An ji ƙarar fashewa a babban birnin Saudiyya

Published

on

An samu rahotannin jin ƙarar fashewa a babban birnin Saudiyya, Riyadh.

 

Wannan na zuwa ne bayan da hukumomin Saudiyya suka sanar da cewa za a dawo da zirga-zirgar jiragen sama a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Sarki Khalid daga jiya Lahadi.

 

An rufe filin jirgin na Sarki Khalid na tsawon makonni biyu bayan jerin hare-haren da mayakan Houthi suka kai akai-akai.

 

Shafin Flightradar, wanda ke bibiyar zirga-zirgar jiragen sama a duniya, ya kuma ruwaito cewa wani jirgin sama ya tashi daga filin jirgin a farkon sa’o’in jiya.

 

Hukumar Saudiyya ba ta bayyana musabbabin sabon fashewar da aka ji a babban birnin ba.

 

Saudiyya, wadda ke jagorantar kawancen soji da ke yaƙi da Houthi, ta ci gaba da kai hare-hare kan yankunan da ƙungiyar ke iko da su a cikin makonnin baya-bayan nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!