Connect with us

Labarai

Mu na sanya ido kan mutane 53 da suka yi mu’amala da ke ɗauke da Ebola- NCDC

Published

on

Hukumar Kula da Cutuka ma su yaɗuwa ta Najeriya NCDC, ta ce ta na sanya ido kan mutane 53 da suka yi mu’amala da matar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola.

 

Babban daraktan hukumar, Dakta Jide Idris, ya bayyana cewa mutane 44 daga cikin waɗanda ake sa ido a kansu suna da alaƙa da cibiyar lafiya da aka kula da mara lafiyar, yayin da aka gano wasu tara a wajen cibiyar, ciki har da ’yan gidanta da ma’aikatan lafiya da suka kula da ita a wani sashen gaggawa.

 

Ya ce adadin ya karu daga mutane 44 da gwamnatin tarayya ta sanar tun farko bayan tabbatar da bullar cutar a Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar ashirin ga watan Oktoba.

 

Dakta Idris ya ce hukumar na ci gaba da bincike da bin diddigin duk waɗanda suka kamu da cutar, tare da tantance mutanen da suka yi mu’amala da su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!