Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti nazarin matsalar karancin man fetur
Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da ta dorawa alhakin nazartar halin matsalar karancin Man Fetur din da ake fama da shi a fadin kasar nan a halin yanzu, da nufin samar da mafitar da za ta kare aukuwar hakan a nan gaba.
Kwamitin wanda zai kasance karkashin jagorancin karamin ministan Albarkatun Mai Ibe Kachikwu, an kafa shi ne bayan kammala taron masu ruwa da tsaki a fannin Mai da iskar Gas a fadar shugaban kasa da ke Villa a jiya.
taron ganawar ya samu jagorancin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya samu halartar shugaban kamfanin main a kasa NNPC Maikanti Baru da babban daraktan tsaro na farin kaya Lawal Daura.
Sauran sune shugaban dillalan mai ta DAPMAN na kasa Dapo Abiodun da takwaransa na IPMAN Chinedo Okonkwo da na kungiyar MOMAN Obafemi Olawore.
A zantawarsa da manema labarai bayan kammala ganawar Ibe Kachikwu ya bayyana cewa kwamitin zai fara aiki nan take, kuma za su yi ganawarsu ta farko a yau Laraba a Ofishin karamain minstan man Ibe Kachikwu.