Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An tsawaita wa’adin rijistar N-Power

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kara wa’adin yin rijista  karkashin shirin baiwa matasa aikin yi na N-POWER zuwa makwanni biyu ta kafar Internet.

An dai fara yin rijista ne a ranar Juma’a na watan jiya na Yuni ya yin da aka kare a jiya Lahadi 26 ga watan nan da muke ciki na Yuli.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mataimakiyar daraktan yada labarai na ma’aikatar dake kula da al’amuran jin kai da dakile Ifita‘ila da kuma cigaban al’umma Mrs Rhoda Ishaku Iliya ta fitar cewa, an kara lokacin ne don baiwa kowa dama don yin rijistar da kuma shawo kan matsalar da aka samu tun da fari.

Ka zalika Mrs Rhoda Ishaku Iliya ta ce kara lokacin ya zama wajibi kasancewar da dama daga cikin wadanda suka nemi yin rijista sun bayyana cewa sun gamu da matsaloli a shafukan Internet akan ya sanya ma’aikatar ta kara wa’adin rufewar.

A saboda haka mataimakiyar darakatan ta yi kira ga matasa masu sha’awar shiga shirin su hanzarta wajen yin rijistar kafin lokacin ya kure.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!