Labarai
Gwamnatin tarayya ta koka kan rashin isar allurar rigakafin Corona cibiyoyin da aka tanada

Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwar ta kan yadda ake samun rahoton rashin isar allurar rigakafin cutar corona zuwa cibiyoyin da aka ware don yiwa al’umma.
Babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta kasa Abdulaziz Abdullahi ne ya bayyana hakan yayin taron kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da cutar corona na gwamnatin tarayya.
A cewar sa rashin aikewa da rigakafin kamar yadda aka tsara zai haifar da koma baya, kuma an shirya cewa za a fara yiwa jami’an lafiya rigakafin a duk inda aka kai.
Abdulaziz Abdullahi ya kuma ce sun samu rahotannin rashin karasawar allurar rigakafin zuwa wasu cibiyoyin da aka tanada.
You must be logged in to post a comment Login