Labarai
Gwamnatin tarayya ta koka kan bullar sabuwar cutar Polio a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwar ta kan bullar sabuwar cutar Polio, a wasu jihohin kasar nan 13 ciki har da birnin tarayya Abuja.
Shugaban hukumar lafiya a matakin farko na kasa Dr Faisal Shu’aibu, ne ya bayyana haka, ya na mai cewa hakan ya samo asaline sakamakon kin karbar magungunan rigakafi da al’umma ke yi.
Dr Faisal Shu’aibu, yace, an samu barkewar sabuwar nau’in cutar ta Polio, ta cVDPV, a jihohin Abia da Bayelsa da Borno da Delta, Jigawa da Kano sai Kebbi da Lagos da kuma Rivers da Abuja.
Haka zalika ya ce an samu bullar cutar a Zamfara da jihar Niger da Yobe sai Borno da Sokoto da suma nau’in sabuwar cutar ta Polio ta fara yawaita a jihohin.
A cewar babban jami’in hakan na zuwa shekara daya bayan da hukumar dake lura da cutar Polio ta yankin nahiyar Afirka (ARCC) ta bayyana kasar nan da cewar ta dakile cutar ta Polio.
Dr Faisal Shuaib, yace hukumar zata hada kai da kungiyoyin duniya dake yaki da cutar tare da daukar matakai na wayar da kan jama’a wajen gannin sun karbi rigakafin.
You must be logged in to post a comment Login