Labarai
Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 16 da kwato makamai

Rundunar sojin kasar nan, ta ce ta kashe ’yan ta’adda goma sha shida tare da kwato wasu makamai, bayan da ta dakile hare-haren da ’yan ta’addan suka kai a wasu sassan Jihar Adamawa.
Rundunar ta ce ’yan ta’addan sun kai hare-hare kusan lokaci guda kan sojojin bataliya ta 226 da ke Garkida, a karamar hukumar Gombi, da kuma bataliya ta 232 da ke Garaha, a karamar hukumar Hong.
Rahotanni sun bayyana cewa, hare-haren sun faru ne da misalin ƙarfe ɗaya na daren ranar Alhamis.
Rundunar ta ce bayan artabun da aka yi, sojojin sun samu nasarar fatattakar ’yan ta’addan tare da kashe 16 daga cikinsu.
Haka kuma, sojojin sun ceto mutane 10 da ake shirin tura wa aikin bautar kasa ta NYSC, wadanda ake zargin ’yan ta’addan sun yi garkuwa da su, tare da kwato makamai da sauran kayan yaki daga hannun ’yan ta’addan.
You must be logged in to post a comment Login