Manyan Labarai
Gwamnatin tarayya za ta rage jinkiri a shari’u- Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga alkalai kan samar da wasu kotuna dan samun sauki wajan gudanar da sharia
Shugaban yayi wannan nan jawabi ne a lokacin da yake ganawa da manyan alkalai na kasa a garin Abuja.
Shugaba Muhammadu Buhari ya fara da bawa kungiyar alkalai ta kasa shawara wajan samar da isassun Kotuna na musamman domin samun sauki wajan gudanar da shari’u da rage yawan cinkoso wajan shari’a .
A wata sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar daga mai bashi shawara akan kafafen yada labarai Mr Femi Adesina yace shugaban yace manyan jami’an harkokin shari’a suna fuskantar matsaloli kuma sun tattauna da babban jojin kasa Ibrahim Tanko Muhammad.
Shugaban ya kara da cewa Gwamnati ta jajirce kan tabbatar da sauye sauye wajan canja wasu dokoki da suke da tsauri da kuma samar da sababbi domin inganta rayuwar ‘‘yan Najeriya.
Bayan haka shugaban yace suna aiki kud da kud da babban jojin kasa wajan tabbatar da kasafin kudin da aka warewa bangaran sharia ya karu domin tabbatar da yayi daidai da bukatun su.