Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya zata yi duba na tsanaki kan kungiyoyi masu zaman kansu
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa zata yi duba na tsanaki kan kungiyoyi masu zaman kan su a kasar nan don tattara bayanan su, sanin adadain su don dakatar da wadanda basa gudanar da ayyukan su kamar yadda ya kamata.
A yan watannin da suka gabata ne dai kudurin dokar yin gyara kan yadda kungiyoyin ke gudanar da ayyukan su, ya gaza tsallakewa a majalisun kasar nan.
Gwamnatin tarayya ta kuma bayyana cewa hakan ya biyo bayan kokarin gwamnatin na tsaftace yadda kungiyoyin ke gudanar da ayyukan su, da kuma dokar da ta hana halarta kudaden haramin da kuma ta’addanci a kasar nan.
Babban Daraktan bangaren binciken masu ta’ammali da Kudaden haramin Francis Usani shine ya bayyana hakan a yayin wani taron kara wa juna sani kan yaki da halasta kudaden haramin da kungiyar da ke yaki da halasta kudaden haramin ta Nahiyar Afrika watau GIABA ta shirya jiya a Abuja.
Mr. Usani wanda kuma shine wakilin kungiyar a Nan Najeriya ya bayyana cewa yin gyara kan kungiyoyin zai taimaka musu tare da kara karfafa ayyukan su.