Labarai
Gwamnatina ba za ta biya kuɗin fansa ko kuma yin sulhu ba- Shugaba Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce, gwamnatinsa ba za ta biya kuɗin fansa ko yin sulhu da masu garkuwa da mutane ba, domin hakan na ƙara ƙarfafa ayyukan ta’addanci da ƴan bindiga.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne yayin karɓar baƙuncin sarakunan gargajiya daga jihar Oyo a Abuja, inda ya ce gwamnatin tarayya ta ƙi amincewa da buƙatar masu garkuwa da ɗalibai da malamai 44 da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo, waɗanda suka nemi kuɗin fansa da kuma sakin wasu daga cikin abokan aikinsu da ke tsare.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na ƙarfafa tsarin tsaro tare da goyon bayan kafa rundunar ƴan sandan jihohi domin magance matsalolin tsaro a ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login