Labarai
Gwamnnatin Kano ta shawarci manoma dasu kalli noma a matsayin riba
Gwamnatin jihar kano ta bukaci manoma dasu kalli noma a matsayin don riba, bawai don ci ba kawai.
Mataimakin gwamnan jihar Dr.Nasiru Yusuf Gawuna ya bukaci hakan a lokacin da yake kaddamar da sabon ofihin hadadiyar kungiyar manoma ta kasa dakuma rabon kayan aikin noma ga wasu manoma a Abuja babban birnin Najeriya.
Yace la’akari da kasar noman da Allah ya huwa cewa kasar to kuwa ya kyautu manoman suyi amfani da wannan albarka wajen yin noman da zai taimakawa tattalin arzikin kasar.
Yadda aka sami arangama tsakanin manoma da makiyaya a Jigawa
Ambaliyar ruwa ya janyo asara ga manoman shinkafa – Kungiya
RIFAN za ta tallafawa manoman da ambaliyar ruwa ta shafa a Kano
Tun da farko dayake jawabi shugaban hadadiyar kungiyar manoma ta kasa Alhaji Faruk Rabi’u Mudi, yace shi da mambobin kungiyar na da burin ganin kasarnan ta dogara da fannin noma da samar da ayyukanui dakuma bunkasa tattalin arziki.
Yace kungiyar da hadin gwiwar ma’aikatar noma ta tarayya za su shirya wani ga-garumin taron manoma da zai hada masu fada aji a fanin na noma, domin tsara manufofin da zasu dora kasar a kan tafarkin noma mai dorewa.
You must be logged in to post a comment Login