Labarai
Gwamnoni sun gana da kwamitin tattalin arziki don shawo kan tsadar rayuwa
Ana sanya ran Gwamnonin jihohin kasar nan 36 zasu tattauna da wakilan kwamitin koli kan tattalin arziki don lalubo hanyoyin magance matsalolin da jihohi ke fuskanta ta fuskar tattalin arziki sakamakon annobar Covid-19.
A yayin taron dai gwamnonin za kuma su tsara yadda taron majalisar kolin kan tattalin arzikin zai kasance, wanda aka tsara gudanarwa a ranar 26 zuwa 27 ga watan Oktoba mai zuwa.
Jami’in yada labarai na kungiyar gwamnonin kasar nan, Abdulrazaque Bello Barkindo ne ya tabbatar da hakan ta cikin sanarwar da ya fitar, yana mai bayyana cewa za’a gudanar da taron ne ta kafar Internet wanda za’a fara da misalin karfe biyu na gobe Laraba 16 ga watan da muke ciki na Satumba.
Barkindo ta cikin sanarwar ya kuma kara da cewa, bayanin abinda za’a tattauna da sauran tsare-tsare na cikin katin gayyata da darakta Janar na kungiyar Asishana Bayo Okauru ya aikewa da kowanne gwamna.
You must be logged in to post a comment Login