Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan sanda a Bauchi sun yi holen wasu mutane da ake zargin su da cin zarafin mata

Published

on

Jami’an ‘yan sanda a jihar Bauchi sun yi holen wasu mutane 15 da ake zargin su da cin zarafin wasu ‘yan mata kanana cikin su har da wasu guda 4 da suka boye wata yarinya ‘yar shekaru 14 tsahon watanni, inda suka rika yi mata fyade ba kakkautawa.

Mutanen sun hadar da Usman Adamu dan shekaru 20 da Adamu Muhammad mai shekaru 21 sai Nura Musa mai shekaru 20 da kuma Khalid Abdullahi wadanda dukannin su ‘yan asalin yankin Nasarawa ne a karamar hukumar Misau.

Tuni dai jami’an tsaro suka mika yarinyar babban asibitin Misau don bata kulawar gaggawa, inda kuma tuni mutanen suka amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce bayan wadannan mutanen an kuma sake holen wasu mutane uku da ake zargin su da hada kai da kuma yiwa wata karamar yarinya ‘yar shekaru 9 fyade a tsahar mota ta Gamawa.

Mutanen sun hadar da Abdullahi Adamu dan shekaru 25 da kuma Abdullahi Abubakar mai shekaru 23 sai kuma Auwalu Haruna dan shekaru 22, inda suma tuni suka amsa laifin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!