Labarai
Gwamnoni za su fara biyan sabon mafi karancin albashi-Kayode Fayemi
Kungiyar gwamnonin kasar nan ta sake nanata aniyarta na cewa nan bada dadewaba gwamnonin kasar nan za su fara biyan mafi karancin albashi na naira dubu talatin ga ma’aikata.
Shugaban kungiyar gwamnonin Kayode Fayemi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai jiya a birnin tarayya Abuja, a yayin wani zaman tattaunawa da gwamnonin suka gudanar.
Kayode Fayemi ya kuma karyata zargin da kungiyoyin kwadagon kasar nan keyi na cewa da yawa daga cikin gwamnonin ba za su iya biyan mafi karancin albashin ba na naira dunu talatin ga ma’aikatan jihohin nasu ba.
Kungiyar kwadago ta kasa na nan kan bakanta na tsunduma yajin aikin gama gari
Muna bukatar Karin albashi ba nazarin albashi ba- Ngige
‘Yan Najeriya na fuskantar karancin abinci – kungiyar FAO
Shugaban gwamnonin Kayode Fayemi ya kuma ce tuni aka cimma matsaya tsakanin gwamnonin kan yadda za’a fara biyan ma’aikatan mafi karancin albashin nan bada dadewa ba.
Ya kuma ja hankalin kungoyoyin ma’aikatan kasar nan da su kaucewa duk wata jita jita dake nuna cewar gwamnonin ba za su iya biyan mafi karancin albashin ba.