Labarai
Gwamnonin Arewa maso gabas sun nemi Buhari ya kara zage dantse wajen yaki da Boko Haram
Kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin kasar nan ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kara azama a yaki da ta ke da kungiyar Boko Haram.
Gwamnonin sun yi kiran ne yayin taron kungiyar gwamnonin arewa maso gabas da ya gudana a jiya Asabar a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Borno Mallam Isah Gusau, ya shaidawa manema labarai cewa, a yayin taron, gwamnonin sun cimma matsaya a kan batutuwa da dama, ciki har da bukatar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samar da karin makamai na zamani ga sojojin da ke yaki da ayyukan ta’addanci.
Sannan sun bukaci suma ‘yan sanda a samar musu makamai na zamani domin taimakawa sojoji wajen yaki da kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin.
A yayin taron dai gwamnonin sun kuma zabi gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum, a matsayin sabon shugaban kungiyar ta gwamnonin yankin arewa maso gabashin kasar nan.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hadar da mai masaukin baki, gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum da gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, da Bala Muhammad Abdulkadir na jihar Bauchi, da kuma gwamnonin Yobe da Taraba da suka tura da wakilci.
You must be logged in to post a comment Login