Labarai
Gwamnonin kasar nan sun bukaci a samar da dabarun tsaro a kasa
An kammala taro kan harkokin tsaro tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin kasar nan wanda aka fara a jiya Talata tare da cimma yarjejeniyar samar da dabarun bunkasa harkokin tsaro don kawo karshen matsalar ayyukan ta’addanci.
Taron ya kuma bukaci manyan hafsoshin tsaron kasar nan da su fito da matakan kare ‘yan kasa musamman ta hanyar hadin kai da al’ummar yankunan don bunkasa tsaro.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa, duk da zaman an yi shi ne ta kafar sadarwa tsakanin gwamnonin da shugaban kasa, sai dai gwamnonin sun bayyana damuwar su matuka kan yadda tsaro ya tabarbare.
Kazalika sun koka kan yadda talauci da rashin aikin yi, yayi katutu a tsakanin matasa wanda ke zama barazana, inda suka ce, akwai bukatar daukan matakan kawo karshensu cikin hanzari.
You must be logged in to post a comment Login