Labarai
Gwamnonin PDP muna goyon bayan sake fasalta Najeriya – Tambuwal

Gwamnonin jam’iyyar PDP sun goyi da bayan sake fasalta kasar nan don dakile matsalolin tsaro.
Gwamnonin sun dau wannan mataki ne yayin wani taron sirri da suka gudanar a yau litinin a Ibadan babban birnin jihar Oyo.
Haka zalika gwamnonin na PDP sun kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fara shirye-shiryen samar da ƴan sandan jihohi don magance matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.
A yayin tattaunawar rahotanni sun ce gwamnonin sun tattauna al’amuran da suka shafi tabarbarewar tsaro da kuma koma baya da tattalin arzikin kasar nan ke fuskanta a wannan lokaci.
Matsayar gwamnonin na PDP na cikin wata takardar bayan taro ne mai dauke da sa hannun shugaban ƙungiyar gwamnonin na PDP kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
A bangare guda gwamnonin na PDP sun goyi bayan matakin da takwarorinsu na kudu suka dauka na haramta kiwo da makiyaya ke yi barkatai a yankunansu.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da: Aminu Waziri Tambuwal, (Sokoto), Udom Emmanuel, (Akwa Ibom), Douye Diri, (Bayelsa), Samuel Ortom, Benue State da kuma Ifeanyi Okowa na jihar (Delta).
Sauran sune: Ifeanyi Ugwuanyi, (Enugu), Nyesom Wike, (Rivers), Seyi Makinde, (Oyo), Ahmadu Fintiri, (Adamawa) da kuma Godwin Obaseki na jihar (Edo).
You must be logged in to post a comment Login