Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwanmatin Nijeriya ta bayyana aniyarta ta cika wa NLC da TUC alkawura

Published

on

Gwamnatin Nijeriya ta ce tana cigaba da yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ganin ta cikan alkawuran data daukarwa gamayyar kungiyoyin kwadago na NLC da TUC.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Nkeiruka Onyejeocha ne ya bayyana hakan da yammacin jiya Juma’ah, inda yace gwamnatin tarayya bata da niyyar kin cika alkawuran data dauka a yarjejeniyar data cimma da gamayyar kungiyoyin.

Onyejeocha ya bukaci kungiyoyin da su maida wukar, la’akari da yadda gwamnatin tarayyar ke cigaba da fafutukar magance tarin matalolin da suka dabaibaye kasarnan.

A cewar sa bukatun da aka cimma yarjejeniyar a kan su, ba bukatu ne da za’a iya cimma su lokaci guda ba, a don haka akwai bukatar kara bada lokaci, a yayinda gwamnatin ta kudiri aniyar biyan bukatun sannu a hankali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!