Labaran Kano
Gwmantin Kano ta musanta yunkurin sauya wa sarkin Kano Masarauta
Sakataren yada labarai na gwamna Kano Abdullahi Ganduje ,Abba Anwar ya musanta rade-raden da ake yadawa cewar gwamnatin Kano na shirin yunkurin sauya wa sarkin Kano Muammadu Sunusi na II masarauta zuwa masarautar Bichi, yana mai cewar labarin bashi da Tushe ballantana makama.
Tun da farko dai wata gamayyar kungiyoyi ce ta yi wannan zargin cewa, sun gano gwamnati na kokarin mayar da sarkin kano Muhammadu Sunusi 11 daga masarautar Kano zuwa masarautar Bichi.
Wannan na kunshe ne cikin wata takarda da mai dauke da sa hannu shugaban gamayyar kungiyar ta Renaissance Ibrahim A Waiya ya sanya hannu yana mai cewar gwamnatin Kano na wannan yunkurin kuma da zarar sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya bijiri za’a tsige shi.
Ibrahim Waiya ya ce wannan yunkuri ba abinda zai haifar illa rashin zama lafiya da tada zaune tsaye da zarar an tabbatar da hakan, ya kara da cewa wannan yunkuri da gawman Kano ke na nuna rashin jituwa a tsakanin sa da sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II.
Shugaban kungiyar ya ce ya zama wajibi kungiyar su ta fadakar da alumma dangane da yiwuwar hakan , domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma, tare da kira ga gwamantin tarayya da ta ja hankalin gwamna Kano tare da hana shi tabbatar da kudirinsa na sauya wa sarkin Kano masarauta.