Labaran Kano
Hadi Zarewa ya bayyana hanyoyin da za’a magance matsalar tsaro
Tsohon Sufeton ‘yan sanda, Muhammad Hadi Zarewa, ya bayyana karancin kayan aiki da rashin kikakken horo da hadin kai da kuma rashin kayan aiki na zamani suka sanya jami’an tsaro suka gaza magance matsalar tsaro a kasar nan.
Muhammad Hadi Zarewa ya bayyana hakan ne a yau ta cikin shirin Duniyar Mu A Yau na nan gidan Freedom Rediyo da ya maida hankali kan lalubo hanyar magance matsalar tsaro a yanzu.
Ya ce, idan aka duba a bangaran masu ayyukan tada kayar baya da masu yin garkuwa da mutane da kuma barayin shanu, na kara ta’azzarane sakamakon talauci da rashin aikin yi da kuma tsadar rayuwa da a ke fama da su musamman a arewacin Najeriya.
A nasa bangaran, tsohon mejon sojin kasar nan mai ritaya Muhammad Tukur Umar, ya bayyana rashin hadin kai tsakanin jami’an tsaro tare da nuna banbanci musamman a bangaran sojoji a matsayin babbar matsalar da ke kara haifar da rashin samun nasara kan yaki da ayyukan ta’addanci a kasar nan.
Haka zalika, ya ce ana samu koma baya a fan in tsaro a Najeriya tun daga lokacin da a ka fara mulkin farar hula sama da shekaru Ashirin da su ka gabata bisa sakacin shugabannin mu da kuma rashin maida hankalin jami’an tsaro na farin kaya wajan samarwa da kuma alkinta muhimman bayanai da suka shafi tsaro a cikin gida da na waje.
Jami’an tsaro ku kama duk mai tunzura jama’a-Sarkin musulmi
Kano ba ta bukatar kafa rundunar tsaro -Ganduje
Takaita amfani da layukan waya zai karfafa tsaro- Hadi Zarewa
Wakilin mu Anas Mande ya rawaito cewa, Muhammad Tukur ya ce mafi yawancin kudaden da a ke warewa don samarwa da jami’an tsaro kayan aiki, ba a alkinta kudaden yadda ya kamata saboda rash in bibiya da gwamnati ba ta yi, inda ya ce ya kamata gwamnati ta ci gaba da bibiyar kudaden da ake warewa bangaran tsaro don samun zaman lafiya a kasa baki daya.
Shi kuma, Honarabul Amanallahi Ahmad Muhammad mai sharhi kan al’amuran ci gaban kasa, ya ce, daya daga cikin hanyoyin da za a bi wajan magance matsalar tsaro sai gwamnoni da sarakuna da manyan yan kasuwa da masu hannu da shuni da Kuma jami’an tsaro, sun hada karfi da karfe tare da cire son zuciya sannan za a iya lalubo hanyar kawo karshen matsalar tsaro.