Manyan Labarai
Hanan Buhari: Sana’a Maganin zaman banza
Daga Abdullahi Isa
Hanan Muhammadu Buhari, ”Ya” ce ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Kuma ‘yar auta kasancewar ta, ita ce ‘Yarsa’ ta karshe.
Hanan dai matashiya ce hazika wadda a kwanan nan ta kammala Digiri a fannin nazarin daukan hoto a wata Jami’a da ke Burtaniya, Kuma ta kammala da Digiri mai daraja ta daya wato ‘First Class’
A karshen makon jiya sunan Hanan ya karade kafafen yada labarai sakamakon wata ziyara da ta kai jihar Bauchi wajen wani taro na gargajiya da aka gayyaceta. Ko da ya ke da dama daga cikin bayanan da aka yada kan wannan matashiya, ya mai da hankali ne kan amfani da ta yi da jirgin shugaban kasa wajen kaiwan ziyarar, wanda wasu jama’a da dama su ke ganin hakan ba daidai bane tun da dai ita ba Jamiar gwamnati bane.
To ni dai wannan ba shine bangaren da na duba ba, sakamakon fuskantar da na yi na cewa kafafen yada labarai sun bar wani muhimmin bangare na ziyarar da Hanan ta Kai jihar Bauchi, wanda shine a wajena labari da ya kamata ya zama abin yadawa.
Ba ko shakka batun sana’a a kasar nan da rashin aikin yi lamari ne da kullum ke janyo cece-kuce yayin da wasu ke ganin laifin gwamnati ne wajen rashin samar da aikin yi gq matasan kasar nan, wasu ko gani su ke laifin matasan ne wadanda su ka gwammace zaman tumasanci da jagaliyanci mai makon yin sana’a da za su rufa wa kansu asiri da iyalansu.
Kwarai da gaske jama’a da dama a kasar nan suna zargin matasa da lalaci da raina sana’a wadanda suke ganin shine dalilin da ke kara taazzara rashin aikin yi. To koma menene gaskiyar Wannan lamari, Hanan Muhammadu Buhari ta zama misali ga matasa wajen nuna muhimmancin da sana’a ke da shi. Ba ko shakka wannan matashiya ta nunawa matasa cewa komi kankantar sana’a matukar Mutum ya rike ta da muhimmancin tabbas zai ci gajiyarta.
Haka zalika wannan bangare na sana’a ta daukar hoto da Hanan ta zaba zai kara karfafa gwiwa da matasa musamman mata su rungumi wanann sana’a wajen samun rufin asiri.
Haka kuma sana’ar matukar mata su ka rumgumeta hannu bibiyu zai kara tsaftace yadda sana’ar ke wakana musamman inda maza zasu daina cakuduwa da maza a lokacin bukukuwa.
Bugu da kari, Hanan ta zama farin wata sha kallo tsakanin matasa wanda za ta zamo misali ga matasa, inda masu hankali daga cikinsu za su fahimci cewa, duk kankantar sana’a tana da matukar tasiri Kuma rufin asiri ne matukar aka riketa da muhimmanci.