Labarai
Hanyar da Diago Simeone ya bi wajen fitar da Liverpool a Champion
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Atlentico Madrid Diago Simeone yayi amfani da ‘yan wasa a baya wajen hana kungiyar kwallon kafa ta Liverpool sakat a zagayen kungiyoyi 16 a Champion League.
Cire Liverpool na nufin kungiyar ta Atlentico Madrid za ta iya daukan gasar cin kofin zakarun na turai duba da yadda tayi waje da mai rike da kambun gasar Liverpool a daren jiya.
Diago Simeone dai yayi amfani da ‘yan wasan sa a baya ta yadda ya hana ‘yan wasan kungiyar ta Liverpool damar matsar mai tsaron ragarsa.
Hakan ya sa masu hasashe yin duba kan yadda kungiyar ta Atlentico Madrid ta iya tattaki har filin wasa na Liverpool Anfil tayi nasara a kanta daci 3-2 jumilla ya sanya tana da kwallo 4 in aka hada da kwallo 1 da taci Liverpool a gidanta inda ita kuma Liverpool din keda kwallo 2.
Ba kasafai ba dai kungiyoyi kan shiga filin wasan Anfin na Liverpool ba kuma har su samu nasara a kansu.
Zuwa ‘yanzu dai Atletico Madrid ta tsallaka zuwa zagayen daf dana kusa da karshe a gasar ta Champions.
Dan wasan Liverpool Georginio Wijnaldum ne ya fara zura kwallo a raga cikin minti na 43 kafin tafiya hutun rabin lokaci.
Hakan ya sanya ‘yan wasan Liverpool suka samu kwarin gwiwa ganin cewa sun dawo wasa inda ya zamana kowacce kungiya na da kwallo daya, duba da atlentico madrid ta cita kwallo daya a gidanta.
Bayan cikar mintina 90 da wasan ne ya sanya akayi Karin lokaci na minti 30 domin a fitar da gwani.
Roberto Firmino ne ya fara jefa kwallo a raga cikin karin lokacin da aka yi a minti na 90 da 4.
Yayin da dan wasan Atletico Madrid Marcos Llorente ya farkewa kungiyar tasa duka kwallaye biyun da aka zura mata a mintuna na 90 da 7 da kuma mintuna na 10 da 5.
A dai-dai lokacin da Liverpool ta fito neman kwallo ido a rufe abin da ya bai wa Alvaro Morata damar tamfatsa kwallo ta uku a ragar LIverpool.
Yanzu dai Liverpool tayi waje a gasar ta Champions sai dai zata iya daukan gasar Premier ta Ingila idan taci wasanni biyu nan gaba.
Wanne fata kuke dashi da kungiyar ta Atlentico Madrid?
You must be logged in to post a comment Login