Kiwon Lafiya
Har yanzu ana ci gaba da binciken asalin corona – WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, har yanzu tana kan bakanta na ci gaba da bincike kan asalin samuwar cutar Korona da ta yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin mutane tare da kassara tattalin arziƙin ƙasashe da dama.
Tuni Majalisar ɗinkin duniya ta ce, alhakin gudanar da binciken na kan masana kimiyya, inda ta ce, magance sake barkewar cutar ya ta’allaƙa ne idan an yi binciken.
Tuni tawagar hukumar lafiya ta duniya ta isa birnin Wuhan don ci gaba da binciken, duk kuwa da yadda China ke kokarin yi wa shirin ƙafar ungulu, a cewar WHO.
Najeriya ce ƙasa ta 4 a yaƙi da cutar corona a duniya – WHO
Ƙwararru sun zargi cewa cutar ta samo asali daga birnin Wuhan, sakamakon cin naman jemage, yayin da zarge-zarge suka fara ɓulla kan cewa an ƙirƙiri ƙwayar cutar a ɗakin gwaje-gwajen ƙwayoyin hallita.
You must be logged in to post a comment Login