Connect with us

Labarai

Har yanzu ba a sako Yunusa Yellow ba

Published

on

Dangin matashin nan Yunusa Dahiru wanda aka fi sani da Yunusa Yellow da ke tsare a jihar Bayelsa, sun ce har yanzu ba a sallamoshi daga gidan gyaran hali ba.

A farkon makonnan ne ake yada labarin cewar wani sanata a nan Kano ya shiga cikin lamarin har kuma yayi sa’ar karbo Yunusa Yellow daga inda yake tsare.

Sai dai ‘yar uwar Yunusa Yellow din mai suna Fatima Dahiru ta shaidawa Freedom Radio cewa har zuwa yanzu Yunusan bai samu shakar iskar ‘yanci ba.

A shekarar 2015 ne dai iyayen wata budurwa Ese Oruru suka yi zargin Yunusa Yellow da yin garkuwa da ‘yarsu, tare da kai ta jihar Kano, inda ya aure ta, har ma aka samu juna biyu.

A watan Mayun da ya gabata ne wata kotu da ke birnin Yenagoa a jihar Bayelsa ta yanke wa Yunusa Yellow daurin zaman gidan kaso na shekara 26 bisa samun sa da laifin safara da cin zarafin Ese Oruru.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!