Labarai
Har yanzu ba a samu hanyar tuntubar wadanda suka sace masu ibada a jihar Neja ba

Gwamnatin Jihar Niger ta ce har yanzu ba ta samu wata hanyar tuntubar wadanda suka sace masu ibada a jihar ba, kwanaki shida bayan harin da aka kai yayin sallar Juma’a.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Obed Nuhu, ya ce har yanzu gwamnati ba ta tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba.
Ya ce harin na ranar 21 ga Agusta ya faru a wurare uku daban-daban a Karamar Hukumar Borgu, kuma ana zargin mayakan Lakurawa da Boko Haram ne suka kai shi.
Kwamishinan ya ce gwamnati na ci gaba da tattara bayanai, don haka ba za ta yi amfani da alkaluman da ba a tabbatar da su ba.
Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun kai hari kan masu ibada a masallacin Kpenya da ke Gidan-Zana, inda suka sace mata da yara da kuma tsofaffi.
You must be logged in to post a comment Login